Additionally, paste this code immediately after the opening tag:

Littafin Hikayoyin Shehu Jaha

Assalamu Alaikum, Ga masu son karanta MANHAJJAR HIKAYOYIN SHEHU JAHA na Tijjani M. Imam ga dama ta samu. ...

Free

Store review

Assalamu Alaikum,

Ga masu son karanta MANHAJJAR HIKAYOYIN SHEHU JAHA na Tijjani M. Imam ga dama ta samu. Wannan manhajja kyautace kuma tana aiki nan take. Bata bukatar a kunna data domin tayi aiki.

Kadan daga cikin Hikayoyin:
- JIFAN GAFIYAR BAIDU
Shehu Jaha ya gamu da wata mace kan hanya. Sai ta tambaye shi daga ina ya fito? Sai yace da ita daga jahannama. Da jin haka
sai ta tambaye shi ko ya ga yaron ta da ya rasu a can? Sai yace da ita ya gan shi a tsaye a kofar Aljanna an hana shi shiga har sai an
biya masa bashin da yake kansa. Sai matar ta bashi kudin da zasu biya wannan bashin, ta kama hanya ta tafi gida, ta bawa mijinta
labarin abin da ya faru, sai nan da nan mijin nata ya zabura ya hau dokinsa don ya kamo barawon. Ko da shehu ya hango shi, sai yayi
wuf ya fada wani gida da ake yin nika, yace da mai nika, don Allah ka cece ni wani Azzalumi ne ya biyo ni, saboda haka
taimakon da zaka kayi mini shine ka karbi rigata ka sanya, ni kuma ka bani taka na sa, sai ka hau wannan bishiyar ka buya a cikin
rassanta. Sai mai nika ya amince da wannan bukata, da mai gida ya iso gidan nika ya shiga, ya tambayi inda barawon yake, sai shehu ya nuna masa mutumin da yake kan
bishiya, nan da nan sai mutumin ya cire GWADONSA ya bar dokin sa, ya hau bishiya don ya kama barawon, sai fa Shehu ya dauki
gwadon ya yi maza ya dare dokin ya sheka a guje. Bayan nan sai mai doki ya dawo gida a kasa, ya ce da matarsa babu shakka mutumin
nan daga lahira yake kuma can zai koma, saboda haka na ba shi mayafina da dokina na ce ya hada da kudin da kika ba shi ya kai
wa yaron...

Godiya ta musamman ga Malama Aisha Bashir wacce ta taimaka sosai domin ganin wannan manhajja ta hikayoyin shehu jaha tazo gareku.

Last update

Nov. 26, 2019

Read more